(ABNA24.com) Shugaban kasar Iran Hujjatul Islam Dr Hassan Rouhani ya bayyana cewa kasarsa ba za ta taba amincewa a keta hurumin kudurin kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya dangane da yarjejeniyar shirin nukliyar kasar ta shekara 2015 ba.
Shugaban ya bayyana haka ne a taron majalisar ministocin kasar a jiya Laraba a nan birnin Tehran. Ya kuma kara da cewa hakkin kasar Iran ce ta saya ko ta seyar da makamai don kare mutanen kasar.
Dr Rouhani ya kara da cewa kudurin kwamitin tsaro na MDD na 2231 bangare ne wanda ba za’a raba shi da yarjejeniyar shirin nukliyar kasar wacce aka fi sani da JCPOA.
Shugaban ya ce kasashe 4+1 wato Rasha, Ingila, Faransa da China game da kasar Jamus, sun san mummunan sakamakon abinda zai biyo baya, idan sun ki amfani da wannan kudurin.
A cikin watan Octoba na wannan shekarar ne kudurin kwamitin tsaro na MDD mai lamba 2231 ya amince a dagewa kasar Iran takunkuman saya da seyar da makamai, amma a halin yanzu gwamnatin kasar Amurka tana sama da kasa don ganin an tsawaita wannan takunkumin.
/129
9 Mayu 2020 - 06:29
News ID: 1034839

Shugaban kasar Iran Hujjatul Islam Dr Hassan Rouhani ya bayyana cewa kasarsa ba za ta taba amincewa a keta hurumin kudurin kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya dangane da yarjejeniyar shirin nukliyar kasar ta shekara 2015 ba.